Amazing

An sayar da zanen Yesu Almasihu sama da N150b
16 Nuwamba 2017
Aika wannan shafi Facebook  Aika wannan shafi Twitter  Aika

Image caption
A shekarar 1958, dala sittin aka sayar da zanen yayin wani gwanjo a London
An sayar da wani zane wanda gwani, dan asalin Italiya, Leornardo da Vinci ya ƙaga a wani gwanjo cikin birnin New York, kan dala miliyan 453 kwatankwacin sama da naira biliyan 150.
Shi ne kudi mafi tsada da aka taba sayen wani zane a duniya.
A gwanjon na tsawon minti 18, jami'ai sun kasa zaune sun kasa tsaye, lokacin da suke sauraron tayi daga masu bukata ta wayar tarho.
Yayin da aka rika ninninka kudin da ake sa ran sayar da zanen.
An dakata kan tayin dala miliyan 400, masu gwanjon kuma suka daddale kan farashin da aka sallama.
Ba a da masaniya kan kowane ne ya sayi zanen.
Ana yi wa zanen wanda ke kamanta surar Yesu Kiristi lakabi da 'Mai ceton Duniya'.
Yana daya daga cikin ayyukan fasaha guda 20 da Leonardo da Vinci wanda ya mutu a Alif Hamsin da Sha Tara ya kirkira.

Comments

Popular posts from this blog

ZAKAT AL - FITR

Buhari must support benue anti-grazing law

Today is silly questions asking day