Have faith

WANNAN LABARIN YA GIRGIZA NI MATUQA
==========================
Wani Bawan ALLAH Da Yake Kan Gargarar MUTUWA, Sai Dangi Suka Kewaye Shi Suna
Ta Kuka.
.
Sai Ya Ce:"Ku Tashe Ni Zaune"
.
Sai Suka Zaunar Da Shi Sai Ya Fuskance Su
Ya Dubi Mahaifinsa Ya Ce:"Baba! Me Yasa
Kake Kukan Rabuwa Da Ni???"
.
Ya Ce:"Ina Jimamin Rashinka Da Yadda Zanyi
Da Kewarka Bayan Ka Rasu!"
.
Sai Ya Juya Ga Mahaifiyarsa Ya Ce:"Umma!
Me Yasa Kike Kukan Rasa Ni???"
Ta Ce:"Saboda Zan Shiga Quncin Rayuwar
Rasaka!"
.
Sai Ya Juya Ga Matarsa Kefa Me Yasa Ki
Kuka???
.
Sai Ta Ce:"Zan Rasa Dadin Zaman Da Muka Yi
Gashi Kuma Ban San Hannun Wanda Zan
Fada Ba".
.
Sai Ya Juya Ga 'Yayansa Kufa Me Yasa Ku
Kuka???
.
Suka Ce:"Saboda Zamu Zama Marayu Bamu
San Irin Wahalar Da Zamu Shigaba Bayan
Baka Nan"
.
Don Allah Idan ku Karanta ku dinga yin Like & Comment ko kuma kuyi Share domin 'yan uwan Mu su Amfana.
.
Daga Nan Sai Ya Dube Su Ya Fashe Da
Matsanancin Kuka Gaba Daya Suka Dube Shi
Kai Kuma Me Yasa Ka Kuka???
.
Ya Ce:"Naga Kowa Yana Kukan Rasa Ni Ne
Saboda Bukatar Qashin Kansa.
.
Shin a Cikinku Akwai Wanda Yake Kuka
Saboda Doguwar Tafiyar Dake Gabana???
.
Koko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda
Rashin
Isashshen Guzuri Na???
.
Ko Akwai Wanda Yayi Kuka Don Za'a
Turbudani a Turbaya???
.
Ko Abin Da Zan Tarar Na Mummunan
Hisabi???
.
Ko Ko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda
Tsayuwata a Gaban Rabbil Izzati Bansan Me
Zan Tarar Ba???
.
Daga Nan Sai Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Sai
Sukai Kansa Suka Juya Shi Sai Sukaga Ashe
Har Rai Yayi Halinsa Ya Rasu!.
.
HAQIQA DUNIYA BATA DA TABBAS!
.
YA ALLAH! KASA MUYI KYAKYKYAWAN
QARSHE, YA ALLAH KAYI MANA KARIYA DA
RADADIN FITAR RAI, YA ALLAH KAYI MANA
GAMDA-KATAR A LOKACIN KARBAN
RAYUKANMU YA ZAMA KAMAR NA SALIHAN
BAYINKA CIKIN RUWAN SANYI
ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEN

Comments

Popular posts from this blog

ZAKAT AL - FITR

Magungunan sanyi ingantattu

Sirrin kaza