Juyin juya Hali a kasar zimbabwe

Bayanai game da Robert Mugabe
Karanta bayanai game da rayuwar mutumin da ya mamaye siyasar Zimbabwe tun lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarar 1960.
An haife shi a shekarar 1924
Ya karanci aikin malanta
Ya yi aki a Ghana inda ya hadu da matarsa ta farko Sally Hafron
1964: Gwamnatin Rhodesian ta daure shi
1980: Ya lashe zaben bayan 'yancin kai
1996: Ya auri Grace Marufu
2000: Ya sha kaye a zaben raba gardama kan ikon shugaban kasa da kuma filaye mallakar fararen fata
2008: Ya zo na biyu bayan Morgan Tsvangirai a zagaye na farko na zaben shugaban kasa, amman madugun 'yan adawan ya janye daga zaben da aka yi a zagaye na biyu yayin da ake kai hare-hare kan magoya bayansa
2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin Firayim minista a lokacin da kasar take fuskantar tabarbarewar tattalin azriki
2016: Ya gabatar da takardun lamuni yayin da karancin kudade ya yi kamari
2017: Ya kori amininsa wanda suka dade tare, mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa
11:50
'Grace Mugabe ba ta da tagomashi a jam'iyyar Zanu-PF'
Nick Mangwana, wani wakilin jam'iyyar Zanu-PF a Birtaniya, ya shaida wa BBC cewa shi ma ya samu rahotannin da ke cewa matar Shugaba Robert Mugabe ta bar kasar. Dazu dai wani dan siyasa na jam'iyyar hamayya ya shaida wa BBC cewa matar shugabn kasar ta tsere zuwa Namibiya.
Amman Mista Mangwana ya ce a siyasar Zanu-PF, Misis Mugabe ba ta da wani tagomashi a halin yanzu, yana mai karawa da cewa ita karamar 'yar jam'iyya ce, kuma ikon da take da shi na kasancewa matar Shugaba Mugabe ne.
11:35
Shugaba Zuma na Afirka ta Kudu ya yi magana da Mugabe a gida
Shugaba Robert Mugabe yana cikin koshin lafiya, in ji Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma.
Mista Zuma ya yi magana da takwaransa mai shekara 93, wanda ya ce an tsare shi "a gida," amman yana "lafiya", kamar yadda wata sanar da ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya fitar

Comments

Popular posts from this blog

ZAKAT AL - FITR

Buhari must support benue anti-grazing law

Today is silly questions asking day