Labari me firgitarwa
WANI LABARI MAI FIRGITARWA !
**********************************
Jama'a wani labari ne na ganshi, wani abokina ya turo min shi da larabci amma sai naga kamar zamu amfana da darasin dake cikinsa don haka na fassarashi a takaice, kuma gashi nan zan kawo :
Akwai wani mutumin kirki anan birnin Riyadh wanda bayan ya haddace Alqur'ani Mai Girma kuma ya samu Limancin wani babban Masallaci daga cikin Masallatan garin.
Na kasance ina binsa sallah tsawon shekaru uku, Mutum ne mai fara'a mai sakin fuska. Amma rannan sai naga fuskarsa adaure. Da alamar lallai yana cikin damuwa.
Na ganshi a haka har kusan kwana biyu ko uku. Don haka rannan da aka idar da sallah sai na zauna acikin masallaci har sai da kowa ya fita ya barmu daga ni sai shi, sai na tambayeshi nace : "Don Allah ka gaya min menene dalilin wannan fushin naka".
Sai ya bani amsa yace "Aranar 18-10-1430 (shekaru goma kenan da faruwar abun) bayan na sallaci sallar asubah sai ga wani yaro 'dan kimanin shekara 13 yazo fuskarsa a firgice yace mun "Ya Shaikh kazo da sauri babanmu ne yake nemanka agida".
Yayin da na iso sai na tarar da baban nasu dattijo ne ya haura shekaru 50 aduniya. Sai ya shigar dani wani daki acikin gidansa. Anan naga abun da ya razanani!
Wata yarinya ce budurwa 'yar kimanin shekaru 22 aduniya tana kwance bata da lafiya, tana lullube da mayafi kuma bisa dukkan alamu rasuwa zatayi.
Shi mahaifin ya kirani ne saboda gashi yarinyar tazo gargara (lokacin fitar rai) amma maimakon kalmar shahada WAQA TAKEYI!.
Wata fitsararriyar Waqa ce wacce wani Mawaqin Qasar larabawa mai suna "Rashid Almajid" ya rerata, fassarar amshin waqar shine "Kaichona Qirji yayi Qunci".
Na kasance idan nace mata "Kice LA ILAHA ILLAL LAAH". Sai ta rera baitin waqar nan "WAILAHU DHAQAS SADR" (Ya kaichona Qirji yayi Qunci).
Na sake ce mata "Kice La Ilaha illal Laah". Sai tace "Wailaahu dhaaqas Sadr".
Haka mukayi da ita har sama da awa guda! Ina ta tunasar da ita Allah, ina Qoqarin sanyata ta furta kalmar shahada amma ita kuma tana maimaita baitin waqar nan...
Chan sai mukaji tayi wani eehu da Qarfi tana cewa : "Kar ku barsu su tafi dani!! Kar ku barsu su tafi dani!! Na rokeku!! Wayoo!! WALLAHI gashi nan ina kallon wajen zamana acikin wuta!!.
Wannan ita ce kalmarta ta Qarshe! ta gama shure-shurenta ta mutu! LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM!! (Ya Allah ka kiyayemu daga mummunar cikawa).
Na tambayi mahaifinta ya gaya mun cewa yarinyar nan bata wasa da sallah. Sai dai ita tana yawan Sauraren Waqoqin soyayya ko batsa, kuma bincike ya nuna cewa tana shiga shafukan internet na batsa!
Anan ne Zauren Fiqhu ke jan hankalin Matasa masu bude shafukan batsa, da masu rubuce-rubucen batsa, da masu Uploading din hotunan batsa cewa suji tsoron Allah su tuba su goge wadannan shafukan daga kan internet.
Wallahi idan ba haka, ta yaya zaka samu kyakkyawar cikawa alhali kana taimakawa shaitan wajen dulmiyar da bayin Allah!!
Mutuwar nan zata iya riskarka ko yau ko gobe.(kuma hoton ko rubutun yana nan ba'a goge ba). Kuma Kamar yadda idan ka bar wani aikin alkhairi anan duniya, ladan zai bika har lahirarka za'a rika ni'imtar da Qabarinka ko yaushe duk sanda wani ya amfana da wannan abun, to haka kuma idan ka rubuta wani abu na batsa, ko ka bude shafi ko group din batsa a facebook ko Whatsapp, wallahi zai yi wahala harshenka ya furta kalmar shahada. Kuma duk sanda wani ya karanta batsar da ka rubuta, ko ya kalla, to sai an Qara balbalo maka wata sabuwar azabar acikin Qabarinka..
Ka tuba tun lokaci bai Qure maka ba!! Ka tuba, domin yanzu haka kofar ruba abude take.
Zauren Fiqhu na bukatar duk wanda ya karanta wannan fadakarwa yayi kokari ya sanar da sauran 'yan uwa matasa domin Allah ba tare da chanza komai ba!
Watakil ta dalilinka wasu zasu shiryu! Allah ya shiryemu baki daya. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU

Comments
Post a Comment