President Buharis budget

Buhari zai kashe naira biliyan daya a tafiye-tafiye a 2018
Sa'o'i 2 da suka wuce
Aika wannan shafi Facebook  Aika wannan shafi Twitter  Aika
Hakkin mallakar hotoNIGERIA PRESIDENCY
Image caption
Buhari ya ce yana son amfani da kasafin kudin wajen inganta rayuwar al'umma
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana shirin kashe kimanin naira biliyan daya a badi wajen tafiye-tafiye, kamar yadda daftarin kasafin kudin kasar wanda ofishin kula da kasafin kudin kasar ya bayyana.
Kamar yadda hukumar ta ce shugaban zai kashe naira miliyan 751.3 wajen tafiye-tafiyen kasashen ketare, yayin da zai kashe naira miliyan 250.02 wajen tafiye-tafiyen cikin gida.
Haka zalika daftarin kasafin kudin ya bayyana cewa za a kashe naira miliyan 907 wajen sayen sabbin motoci da kuma sayo kayayyakin gyaransu a shekarar 2018.
Har ila yau za a sayi tayoyin motoci masu silke a kan naira miliyan 83.77 da sauran motoci da motocin daukar marasa lafiya da sauransu.
Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo zai kashe jimullar naira miliyan 301.04 a kan tafiye-tafiye.
Wane bangare Buhari zai fi kashe wa kudi 2018?
Kasafin da Buhari ya gabatar 'bukata ce kawai'
Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2018 na N8.6tr
A makon jiya ne Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.6 ga majalisar dokokin kasar.
A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin naira tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai.
Ya kara da cewa Najeriya tana hasashen cewa za ta sayar da gangar mai sama da miliyan biyu a ko wacce rana.

Comments

Popular posts from this blog

ZAKAT AL - FITR

Buhari must support benue anti-grazing law

Today is silly questions asking day