Nigerian politics

Siyasar Nigeria Yan uwana hakika siyasa a nigeria ta kawo cigaba mai matukar yawa idan muka kalla ta fannoni masu yawa a rayuwar mu. haka kuma dai idan muka dubeta ta ta wata fuskar ta taka muhimmiyar rawa wurin raba kawunan al'umma a kasar. yana da kyau na bayyanarwa da yan uwana cewa hakika ni ba dan siyasa bane sai dai ina da yawan bibiyar abinda ya shafi siyasa. hakika abinda ya faru a wannan kasa ranar 24/01/2018 Ya mutukar bani mamaki. wai mutumin da ya mulki kasarnan tsawon shekaru 8 ba tare da ya tsinanawa kasar komai ba in ban da saida kadarorin gwamnati da rabar da kudin kasar ban da cin hancin da yaringa rabawa sanatoci na wajen naira 50million ga kowanne domin su amince da kudirinsa na komawa karo na uku, uwa uba kuma da karya tattalin kasar banda kudade makudai da aka ware da sunan za'a gyara matsalar wutar latarki. Abin mamakin na gaba shine suna ina lokacin da kasar ta fada economic recession, suna ina lokacin da yan naija delta avengers da ipob suke kokarin hargitsa kasar. suna ina lokacin da mutane suka kasa tsugunno a yanki gabacin arewacin kasar nan. inaso mutane su gane cewa wannan wasika ta tsuhon shugaban kasar nan bata da wani amfani tunda har wancan lokacin daya wuce basu taba fitowa suka bada shawara game da matsalolin kasar ba. baya ga haka inaso mutane su gane cewa tsohon shugaban kasar yayi amfani da kuratowar zabe mai zuwa domin ya janzawa mutane tunanin su domin cimma wasu bukatunsu na siyasa. Amma ban da haka mene na maganar contesting na shugaban kasa da maganar tattalin arziki bayan yasan irin ta adin da jam'iyyarsa ta yiwa tattalin arziki a kasar. daga karshe ina fata wannan magananar bazatayi tasiri a zukatan yan nigeriya ba.

Comments

Popular posts from this blog

ZAKAT AL - FITR

Magungunan sanyi ingantattu

Sirrin kaza