Faithful

```SALLAR ASUBAHI sallah ce mai muhimmanci. Allaah ya rantse da lokacinta a cikin al-Qur'ani.

Allaah yace:-
( والفجر وليال عشر )

👉🏿Saboda muhimmancin ta ne Allaah ya kirata da sunan "QUR'AANUL FAJR"
Allaah yace:-
( أقم الصلاة لدلوك الشمس إلى غسق الليل وقرآن الفجر إن قرآن الفجر كان مشهوداً )

👉🏿 Dan uwa zaka tauye wa kanka lada mai yawa idan baka Tashi kaje ka sallace ta ba.

👉🏿 Zaka rasa darajoji masu dimbin yawa idan ka gagara tashi don sallar ta.

Ka tuna fa itace Sallar da take wa munafukai nauyi

✅ Manxon Allaah (swallallaahu alaihi wa sallam) yace Nafilar asubahi tafi duniya da abinda yake cikin ta.
((ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها))

الله اكــــــــــــــــــــــبر

Idan har raka'atal Fajri tafi duniya da abinda yake cikin ta, toh ya kake ganin ita kanta Sallar Asubahin ??

KANA SON A DASA MAKA BISHIYA  A ALJANNAH?

🌴

Manzon Allah (s.a.w) yace: "Duk wanda yace 'Subhanallah, Walhamdulillah, Wala'ilaha Illallah, Wallahu Akbar', za'a dasa masa bishiya a Aljannah da kowanne daya daga cikin su".
Silsilatul Ahaadiisus Sahiha 2880.

Me kake tsammani bayan ka idar da Sallah ka zauna ka yi ta wadannan zikirorin?
Me kake zaton ma'anar za'a dasa maka bishiya a Aljannah? Idan bishiyar taka ce Aljannar da bishiyar ke ciki fa? Tabbas taka ce.
👏🏻Ya Rabbana duk wanda ya tura wannan har wasu suka karanta suka amfana, Ya Allah Ka dasa masa bishiyoyi  a Aljannah iya adadin mutanen da suka karanta suka amfana a dalilin sa.```

Comments

Popular posts from this blog

ZAKAT AL - FITR

Magungunan sanyi ingantattu

Sirrin kaza