Story exciting
***INA HUJJAR TAKE? (1)***
DUNIYAR MARUBUTA
Nazifi Muhammad > DUNIYAR MARUBUTA
^^^KUNNENKU NAWA?^^^
INA HUJJAR TAKE
Na Matar Nasimat!
Idanunta sun yi jawur kamar jan gauta saboda
tsabar kukan da ta sha, kana kallonta ka san
tana cikin rashin nutsuwa. Yanayin fatarta ma ya
nuna ba haka asalin haskenta ya ke ba.
Tana girgiza kai ta dubi Hajiya Naja'atu da 'yarta
Shafa'u da ke zaune a gefenta, ta ce.
"Mummy, rayuwata tana cikin garari, ku tausaya
min ku ba ni kariya, idan ba haka ba, wallahi gab
na ke da tarwatsewa."
^^SHIMFI'DA 1^^ Like · 2 · Nov 6 at 6:44pm Nazifi
Muhammad ^^SHIMFI'DA 1^^ Idanunta sun yi
jawur kamar jan gauta saboda tsabar kukan da ta
sha, kana kallonta ka san tana cikin rashin
nutsuwa. Yanayin fatarta ma ya nuna ba haka
asalin haskenta ya ke ba. Tana girgiza kai ta
dubi Hajiya Naja'atu da 'yarta Shafa'u da ke
zaune a gefenta, ta ce. "Mummy, rayuwata tana
cikin garari, ku tausaya min ku ba ni kariya, idan
ba haka ba, wallahi gab na ke da tarwatsewa."
Hajiya Naja'atu ta girgiza kai cikin jimami,
sannan ta ce. "Yi shiru haka nan Fulani, duk
wanda ya sanki a da, idan ya ganki yanzu ya san
kina bukatar taimako. Amma matsalar ita ce, tun
d'azun da kika iso gidan nan mun tambaye ki me
ya faru kin 'ki sanar da mu, sai kira kike mu
tausaya miki... Tausayi ai dama ya zama dole ga
dukkan musulmi matsawar yana da karfin imani...
Shin yaushe kika baro Egypt? Kuma mene ne ya
hana ki je gidanku?" Wasu hawayen suka 'kara
zubo mata, tana girgiza kai ta ce. "Mummy dubi
yadda na koma, na rasa gata a duniya, ina zan
saka kaina?" Shafa'atu ta dube ta, ta ce. "Don
Allah Fulani ki nutsu ki bamu amsa, don musan
yadda zamu hudowa lamarin." Shiru bata amsa
ba, sai da taci kukanta, sannan ta fyace majina
ta ce.
BIYU. "mummy, ina ne kungiyar kare hakkin dan
Adam ta ke?" Gaba dayansu suka fito da idanu
cike da tsananin tsoro, Hajiya Naja'atu ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, me ya yi zafi
haka Fulani? Wa za ki kai 'kara?" Kai tsaye ta
amsa mata. "Daddyna zan kai 'kara!!!" Zumbur
suka mike a matu'kar razane, Shafa'atu ta ce.
"Kina da hankali kuwa Fulani? Mahaifinki za ki
kai 'kara a hukumar kare hakkin dan Adam?"
Fulani ta mi'ke ita ma, ta ce. "Wallahi Mummy,
sai na kai Daddy 'kara ga hukumar kare ha'k'kin
dan Adam, ko da kuwa hakan zai yi sanadin
'karewar numfashina a duniya!!!" Wannan karon
ma idanu suka sake fitowa waje, Hajiya Naja'atu
ta shiga sallallami. "Yau na shiga uku ni Naja'atu,
anya kuwa Fulani kina cikin hayyacinki? Ko kin
fara shaye shaye ne? Me kike so duniya ta dauke
ki, mahaifinki za ki yiwa wannan tozarcin?
Haba..." Fulani ta katse ta da fad'in. "Wallahi
Mummy ina cikin hayyacina, tun da nake
rayuwata ban ta6a shan kayan maye ba. Kuma
Daddy shi ya tozarta kanshi ba ni ba." Kuka ya
sake kwace mata. Hajiya Naja'atu ta tsura mata
idanu kawai ta kasa cewa komai, haka Shafa'atu
sai girgiza kai ta ke kamar 'kadangaruwa. Cikin
kukan Fulani ta ce. "Wallahi ba zan ta6a yafewa
Daddy tozarta min rayuwar da ya yi ba, kuma sai
na bi duk hanyar da zan bi na fitar mana da
ha'k'kinmu a kansa." Hajiya Naja'atu ta ce mata.
"To na ji, zauna sai mu san abin yi." Ba musu
Fulani ta koma ta zauna tana share hawaye.
Shiru na tsayin mintuna goma sannan Hajiya
Naja'atu ta ce. Fulani, bari na yi miki matashiya
akan matsayin mahaifa ga 'ya'yansu. Iyaye su ne
'kashin bayan duk wani d'a da suka haifa, Allah
Ya wajabta yin biyayya a gare su matsawar
biyayyar ba ta sa6awa addini ba. Haka kuma
babu iyayen da za su haifi d'a su so jefa shi
hanyar da zai muzanta, sai dai idan iyayen ba na
'kwarai ba ne. Wannan na yarda za su iya abin
da ya fi haka ma. Akwai ha'k'kok'i masu dama
da suka wajabta ga 'ya'ya da iyaye, wanda a
fahimtar da na yiwa rayuwarki mahaifinki bai
gaza da sauke wad'annan hakkoki a gare ki ba.
Koda ma ya gaza abin da kike shirin yi sam bai
dace ba, domin ya halatta idan d'a ya ga
mahaifansa sun yi wani abu da bai dace da
addini ba ya nusar da su. Ga dukkan alamu kuma
ke ba ki yi haka ba, don me za ki bar wa
shaid'an linzamin zuciyarki?" Ta tsagaita tana
duban Fulani, yayin da Fulanin ta yi murmushin
takaici, ta ce. "Mummy idan da akwai yiwuwar
hakan ba zan ce zan kai Daddy ga hukuma ba.
Abin da Daddy ya yi min ya sa6awa addini,
domin ya keta min HADDI!!!" Jin ta ambaci haka
Hajiya Naja'atu ta san lamarin ya munana, munin
da bai kamata ta tauye Fulanin ba, don haka ta
ja numfashi, ta ce.
UKU. Jin ta ambaci haka Hajiya Naja'atu ta san
lamarin ya munana, munin da bai kamata ta
tauye Fulanin ba, don haka ta ja numfashi, ta ce.
"Shi ke nan, akwai wata aminiyata Hajiya Rashiga
Usman Gidad'o da ke aiki a hukumar kare hakkin
dan Adam da ke Abuja, kin ci sa'a ta zo garin
nan shekaran jiya zasu yi bikin 'kaninta, don haka
ki yi hakuri yanzu dai dare ya yi, ki kwanta ki
huta, inyaso gobe da safe sai mu je gurinta."
Fulani ta goge hawayenta, ta ce. "Shi ke nan
Mummy, na kuma gode." * Misalin karfe goma na
dare Fulani da Shafa'atu na kwance akan gado,
Shafa'atu ta dan juyo ta dubi Fulani tare da
ambatar sunanta. Fulani ta amsa ita ma ta juyo
ta dube ta, Shafa'atu ta ce. "Ina kika baro
Juwairiyya?" Ta ce, "Tana gurin mahaifinta."
Shafa'atu ta girgiza kai, ta ce. "Kin yi kuskure da
kika baro ta, a ganina a matsayin Juwairiyya na
'karamar yarinya 'yar shekaru biyu bai kamata ki
barota uwa duniya haka ba. A tunanina laifin
wani ba ya shafar wani, tunda ba mahaifinta ne
ya 6ata miki rai ba, bai dace ki barshi da
Juwairiyya ba. A tunaninki wane hali za su shiga
su duka biyun yayin da suka rasa ki?" Fulani ta
cije le6e cike da takaici, ta ce. "Wallahi ba ni
sonta... Don Allah mu rufe shafin hirar nan,
zuciyata na tu'ku'ki." Shafa'atu ta yi shiru ba ta
kuma magana ba gudun kar ta kuma sanya
Fulanin a wata damuwar. Washegari da safe sun
gama 'breakfast' karin kumallo har maigidan
Alhaji Nura, sannan Hajiya Naja'atu ta umarci
Fulani da su shirya. Ba su 6ata lokaci ba suka
gama komai, suka fita a motar Hajiya Naja'atun.
Tafiyar mintuna arba'in da uku ta sada su da
Zawachiki Haousin Estate, sun tarar da Hajiya
Rashida a gidanta ba ta tafi gurin hidimar bikin
da suke ba. Kallo d'aya Fulani ta yiwa matar ta
nutsu da yanayinta, ta kuma tabbatar zata iya
taimaka mata. Bayan sun gama gaisawa, Hajiya
Naja'atu ta yi mata bayanin abin da yake tafe da
su. Shiru na wani lokaci Hajiya Rashida ta yi tana
nazari, sannan daga bisani ta dire kallonta ga
Fulani, ta ce. "INA HUJJAR TA KE na kai
mahaifinki ga hukuma da kike yun'kurin yi?"
Fulani ta yi shieu kamar ba ta ce ba, sai kuma ta
ga wannan ita ce fa damar da zata yi amfani da
ita ta ceto rayuwarta daga tarkon da ta ke ciki,
don haka ta ce. "INA DA HUJJA mai 'karfi da ta
sa ni wannan yun'kurin." Hajiya Rashida na
kallonta, ta ce. To zan so jin HUJJAR kafin na
amince miki aiwatar da wannan yunkuri." Ranar
wanka aka ce ba a 6oyen cibi, haka Fulani ta
ambata a ranta, tukunna ta gyara zamanta tana
duban Hajiya Rashida ta soma da cewa. INA
HUJJAR TA KE? "ba ni mantawa da ranar wata
laraba, duk da a lokacin ina da karancin shekaru,
domin ban haurawa shekaru sha biyu ba, amma
kaifin hankali da wayon da nake da su a lokacin
zan iya tunawa da duk wani al'amari da ya
gudana a gareni. Misalin 'karfe goma na dare ne,
mun gama daukar karatu daga Malam Sunusi
Mustapha Isah wanda ya ke koya mana ilimin
addini, gab na ke da soma bacci, don kanwata
Murjanatu mai shekaru hudu tuni ta yi bacci. Ba
zato ba tsammani UMMI ta shigo dakin da sautin
kuka, ga kuma hawaye da ta ke sharewa a
fuskarta. Kai tsaye ta fada saman gado yayin da
na matsa kusa da ita ina fadin. "Ummi me ya
faru?" Ba ta iya ba ni amsa ba, illa ci gaba da
kukanta da ta yi. Abin da ya sa nima na fashe da
nawa kukan ke nan. Haka Ummi ta rungume ni
muna ta kuka ni da ita babu mai rarrashin wani,
har tsayin lokaci sannan na yi lamo akan gado
hawaye na shatato min babu sautin kuka, sai
ajiyar zuciya. Ita kuwa Ummi sam ba ta tsagaita
da kukanta ba, zan iya cewa wani ne ma ke korar
wani. Ko da na ji an turo kyaure ban daga kai ba,
domin ba 'karamin kuka na sha ba. Muryar Daddy
da naji yana kiran. ***
^^4^^ "HALIMATU!" Na tabbatar shi ne ya shigo.
Sanin da na yi da tsare gida, wato ba ya
saurarawa kowa cikin 'ya'yansa ya sa na 'ki dago
kai, shesshek'ar kuka da ajiyar zuciya ma da
nake yi, na yi kokarin tsayar da su. A kalla ya
kira sunan Ummi ya fi sau uku ban ji ta amsa ko
d'aya ba, hakan ya sa na gane kukanta yana da
nasaba da shi ne. Ji na yi ya ci gaba da cewa.
"Don Allah Halimatu ki rufa min asiri, wallahi ba
halina ba ne, ko nawa ne zan ba ki matsawar za
ki rufe sirrina." Wannan karon na jiyo ta ce.
"Kana tunanin akwai amfanin da 'kazamar
dukiyarka zata yi min? Ai wallahi AHMAD ka ba
ni mamaki da kunya, ban ta6a tunanin zan same
ka da zamba cikin aminci ba..." Ya katse ta da
cewa. "Na ro'ke ki da wanda ya busa mana
numfashi ki yi hakuri, ki kuma rufa min asiri.
Wallahi kin ji na rantse na daina har abad..." Ita
ma ta katse shi cikin raunanniyar murya, ta ce.
"Ka daina hada ni da Allah, asirinka kam a rufe
yake kamar yadda ka rufe shi, sai dai ka sani
idan Ubangiji Ya yi nufin tona maka asiri, ni da
kai da abin da ka mallaka ba mu isa rufe shi ba.
Ni dai da bakina babu wanda zan iya fadawa, sai
dai ka sani tsalle daya zaka yi ka fada rijiya,
ma'ana muddin ba ka sauwa'ke wa aurena ba, to
a sauyawar zamana da kai kadai zai iya sanya
wa a asirinka ya tonu." Muryarsa a sanyaye ya
ce mata. "Wannan hukuncin ya yi min tsauri
Halima..." Ta katse shi tun kafin ya karasa.
"Ashe kuwa ba ka fatan asirinka ya rufu? Wallahi
ka ji na rantse da girman Ubangiji, muddin ba ka
sake ni ba, komai zai iya faruwa." Shiru na 'yan
mintoci, sannan na ji ya ce. "Na ji zan sake ki,
amma sai kin yi alkawarin ba za ki fadawa kowa
ba har abada." Murmushin takaici na ji ta yi, ta
dora da fadin. "Na yi alkawari, sai dai Ubangiji na
kallonaka, zai kuma fidda hakkin duk wanda ka
zalunta." Ya ce, "Eh na ji, tunda kin yi alkawari
na gode, ki ba ni kwana hudu insha Allah zan
sauwake miki." Ta ce, "Ina jira, idan kuma ka
rushe hakan ina mai yi maka albishir da kwana
hudu ba zasu maimaituwa ba da izinin Ubangiji
sai ka ga abin da ranka ba zai so ba." Ya ce, "Ka
da ki damu." Ina jiyo takunsa har ya fice daga
dakin, yayin da Ummi ta sake fashewa da wani
sabon kukan. Karancin shekaruna bai hana ni
fahimtar wani gagarumin laifi Daddy ya aikata
wanda ba ya son fallasuwarsa, sai dai na kasa
cankowa a lokacin, domin ban san hanyar da zan
canko din ba. Washegari sam ban ga walwalar
Ummi ba, domin yini ta yi a daki, su Googgo
Zulai dama ba shigowa suke dakin ba, saboda
mummunar akidar zafin kishi da suka sanya wa
ransu. Don haka babu wadda ta damu da rashin
ganin Ummi na zirga-zirga a gidan, musamman
da ya kasance yau kwanakin girkin Ummin ya
kare, Inna Amina ta kar6a. Ni ma hakan ce ta
faru da ni, ko da na je makaranta ma ban sami
nutsuwa ba, har malamai na tambayar ko ba ni
da lafiya ne? Da "Eh" na ke bin su, domin a
hakika ma ba ni da wadatar lafiyar. *** **** ***
Matan mahaifina guda uku ne@ Goggo Zulai mai
yaya uku ita ce uwargida, Yaya Hisham da ke
karatu a Malaysia shi ne babban danta kuma
babba gaba dya a gidan, sai A-Asiya ke bi masa,
sai A-Mardiya. Mahaifiyata ita ce mata ta biyu a
gurin mahaifinmu, sunanta Halimatu wadda muke
kira Ummi, ita ma mu uku ta haifa, Yaya Usman
da Ke karatu a Florida shi ne babba a dakinmu,
sai ni SAFINATU da nake binsa ana kirana da
FULANI, shekaru kusan goma tsakanina da shi.
Mahaifiyarmu ta sake haihuwa abin da ta haifa
baizo da rai ba. Sannnan ta sake 6arin wata
biyar. Bata sake samun ciki ba, sai da na
shekara takwas, sannan ta sami cikin Murjanatu.
Inna Amina ita ce mata ta uku a gurin Mahaifina
Ahmad Lere, an aurota ne gab da za a haifi
Murjanu, a yanzu haka tana da danta namiji guda
daya mai suna Hamza, jimillar yaran gidan mun
tashi bakwai. Ummi tana da hakuri, sai dai yawan
tashin hankulan su Goggo Zulai ya sa ta zabure
tana maida raddin wasu abubuwan da suke mata.
'Mhm!....'

Comments
Post a Comment